Dogon tarihin akan manufar kungiyar Izala a Najeriya

Dogon tarihin akan manufar kungiyar Izala a Najeriya

- An rahoto wani dogon tarihin akan wata kungiya mai suna kungiyar Izala

- Wanna bayani tana akan shafin Facebook din jaridar Rariya akan manufar kafa kungiyar Izala a kasar Najeriya da sauran kasashen duniya

- Dandalin mu na Jibwis Najeriya mun dan waiwaya baya kadan mun gutsuro muku wasu daga cikin manufofin kafuwar kungiyar tun asali.

Wani dogon tarihin ta fara inda take cewa wanda, Wannan kungiya ta al’ummar Musulmi, an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhaji Musa Maigandu Muhammad, a karkashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.

Wannan Kungiya ta addininMusulunci ce, wacce Musulmi suka kafa kuma tana da hedkwata a Jos, Jihar Pilato, sannan tana da ofishin tuntuba a Babban birnin tarayya Abuja, inda anan ne ofishin Shugaban ta na kasa yake a halin yanzu, kungiyar ba ta da alaka ko wace iri ce, da wata kungiyar asiri ko kuma kungiyar Siyasa.

Wannan kungiya tana kan tafarkin Musulunci ne wanda ta dogara ga Qur’ani da hadisan Annabi Muhammad (SAW) bisa fassarar magabata.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Kabiru Gombe ya maganta akan Izalatil Bid’ah

Babu bambanci a cikin kungiyar idan dai har mutum Musulmi ne da ya yi imani da Allah, kamar yadda Annabi

Muhammad (SAW) ya karantar. Kungiya na maraba da irin wannan mutum da kuma shawarwarinsa masu amfani wadanda suka dace da musulunci.

Kungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin Musulunci a

nahiyar Afirka, musamman Nijeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu

ginshikan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga ci.

Dogon tarihin akan manufar kungiyar Izala a Najeriya
Wani tsohon shugaban kafa kungiyar Izala

Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da: Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu; Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW), ba tare da son zuciya ba; Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare; Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka; Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT); Duk wanda ya yi da’awar Annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne; Ya'da Musulunci a Nijeriya da wajen Nijeriya; Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin ki, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani. Kar a boye hujja idan dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).

Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun Hada da: Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Kadan daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:

- Kwamitin Da’awah.

- Kwamitin Ayyuka

- Kwamitin Kula da Marayu

- Kwamitin Ilimi.

- Kwamitin Sulhu da fatawa da ladabtarwa.

- Kwamitin Taimakon Gaggawa.

-Kwamitin Masallatai.

-Kwamitin yada labarai.

-Kwamitin yanar gizo

-Kwamitin Marayu da Gajiyayyu.

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, Khalifa na farko a sashin Shugabancin kungiyar tun bayan kafa ta, wanda tsohon mataimakin

shugaban kungiyar ne bayan rasuwar Marigayi Sheikh Imam Ikara, duk a lokacin a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa Maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne

bayan rasuwar Shugaba Maigandu Muhammad.

- Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe: Shine Mataimakin Shugaban Kungiyar Na Kasa na daya.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Izalatil Bid'ah sun ziyarci Khalifah Tijjaniyya

-Sheikh Abbas Muhammad Jega: Shine Mataimakin Shugaban Kungiya na kasa na biyu.

- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiyar na kasa.

- Sheik Dakta Ibrahim Jalo Jalingo: Shugaban Majalisar Malamai

na kasa.

- Sheik Baristq Ibrahim Sabi'u Jibia: Mataimakin Shugaban

Majalisar Malamai na Kasa.

- Injiniya Mustapha Imam Sitti: Shugaban Rundunar Yan Agaji

na Kasa

- Alhaji Muhammad Kabir Sa'id Gusau: Mataimakin Shugaban

Rundunar Yan Agaji na kasa a bangaren ( Training and Operation)

-Alhaji Abdullahi A. Diggi: Mataimakin Shugaban Rundunar 'Yan Agaji na kasa a bangaren (Finace and Admin).

Kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Nijeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Nijeriya 36 da birnin tarayya Abuja. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Saudi Arabia, Amurka, England, Niger, Kotonu, Mali, Senegal, Togo, Kamaru,

Chadi, Burkina faso, Gini, da sauransu.

Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:

- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.

- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.

- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko Uku ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.

- Kafa makarantu domin koyar da ilmin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.

- Kai Ziyara Zuwa gidajen marayu, fursina da asibitoci, domin tallafawa musulmai marasa galihu.

- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Kungiyar ta samar da hamshakan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilmi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi

Muhammad (SAW), sau da kafa.

Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin Izala zai zo dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Isma'ila Idris Ibn Zakariyya (Shugaban Majalisar Malamai na

farko) ya bayar dan kafuwar wannan kungiya mai albarka ba, da irin su Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa, Marigayi Sheikh Hudu Chikaji Zariya, Marigayi Sheikh Adam Mai Shafi, Marigayi Sheikh Abubakar Imam Ikara, Marigayi Sheikh Musa Maigandu Muhammad da Marigayi Alhaji Ali Ibrahim Tofa (Tsohon

Shugaban 'yan agaji na kasa), koda Kuwa ba manufarmu mu zayyana sunan kowa ba.

Haka su ma kwamitin mutum goma sha hudu da suka tsaya suka bada lokacin su wurin rubutuwa kungiyar kundin tsarin

mulki tun farkon kafa kungiyar har zuwa yau, muna addu'ar Allah ya saka musu da alkairi, wadanda suka rasu Allah ya jikansu da rahama.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Izala ta ziyarci kasuwar Abubakar Rimi

Ga sunayen su:

1.Alhaji Ahmadu gyallesu-zaria

2. Sheikh yakubu musa-katsina

3.Alh. Isa waziri-gombe

4.Sheikh Isma'ila idiris-jos

5.Alh. yaro bichi-kaduna

6.Sheikh hudu cikaji-zaria

7.Alh. Mamman malunfashi-katsina

8.Sheikh Rabi'u Aliyu daura-kaduna

9.Alh. Bashir makama-zaria

10.Sheikh sidi attahir-sokoto

11.Ali ibrahim hikima-jos

12. Sheikh Dr. Alhassan Sa'eed Adam Jos.

13.Alh. Bala Japan-Benue

14. Sheikh Sa'idu Hassan Jingir Jos

Su ma sauran matasan Malaman da a baya suka bada gudunmawar su dan kungiyar ta cimma manufofinta, wanda a yanzu sun zama Dattawa, a farkon tafiya gashin su baki ne, amma yanzu ya rikide ya zama fari sol, kuma ba'a daina yin wa'azin ba, irin su Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam jos, wanda shine Alaramman kungiyar na farko mai jan baki a mambari, yayin yin wa'azi, da Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, wanda a farkon tafiya shine Mataimakin Shugaban Majalisar

Malamai na biyu, Sheikh Rabi'u Aliyu Daura, Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe, Sheikh Abbas Muhammad Jega, Sheikh Sa'idu Hassan Jingir, Sheikh Habibu Yahaya Kaura, Alaramma

Abubakar Adam Katsina, Alaramma Yahuza Bauchi, Alhaji Idris

Zakariyya Mai kaset Jos, da sauran wadanda suke raye ake fafatawa da su a halin yanzu.

Wannan kadan ne daga cikin dan binciken da dandalin mu na Jibwis Nigeria ya gutsuro muku dan mu yi waiwaye mu ga ayyukan matasa a wancan lokacin.

Daga karshe muna addu'a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka ta ci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu da su a babban matsayi a lahira. Amin

Source: Legit.ng

Online view pixel