Manyan Labarai Guda 9

Manyan Labarai Guda 9

Legit.ng ta tattara maku manyan labaran da sukayi fice a ranar Talata 11 ga watan Agusta. Ku duba domin Ku same su.

[article_adwert]

1. Shugaba Buhari ya gana da kwamitin Abdulsalami.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da kwamitin zaman lafiya da tsohon shugaban Kasa Abdulsalami ke shugabanta a ranar Talata 11 ga watan Agusta a fadar shugaban Kasa.

2. Ina Dala Biliya 1 da aka ciyo bashinta domin a yi hanyar jirgin kasa - Buhari.

Shugaba Buhari ya kalubalanci ma'aikatar kudi data gano bangaren Naira Biliyan 1 da aka ciyo bashi domin gina hanyar jirgin kasa.

3. Yan sanda sun kama wata mata wadda ta saida jaririn ta akan Naira 700,000.

Yan sanda sun kama wata mata mai suna Chinwendu Agbo, wadda take  Ehalumona kuma take zama a Obollafor Lodge a Jihar Enugu domin ana zargin ta da saida jaririnta.

4. Wasu hotuna masu gayatarwa daga diyar gwamna Ajimobi.

Daya daga cikin Ya'yan gwamna Ajimobi na Jihar Oyo ta saki wasu hotunan da ake ganin yana cikin shirin bikin da zatayi.

5. Kungiyar hadin kan kasashen  Turai zata taimaka ma matasan Najeriya.

Kungiyar hadin kan kasashen Turai (EU) ta bayyana niyar ta ta taimaka ma Jihar Rivers da samar ma Mata 2,500 aiki a Jihar. Amos Kelsius ko'odinatan State Employment and Expenditure for Results (SEEFOR) ya bayyana hakan.

6. Matatar Mai ta Kaduna zata rage kudin da ake kashewa wajen shigo da mai.

Idan matatar Mai dake Kaduna ta fara aiki a karfinta na kaso 90, sama da Dala Miyan 5.3 za'a ringa adana ma Najeriya kullum. Malam Shehu Malami ne ya bayyana hakan.

7.  Festac Town: wani gari a Legas inda fitsara tayi yawa.

Festac town an gina shine a 1977 domin ya zama wajen da za'a nuna al'adun bakar fata na Afirika. Abun takaici, yanzu garin ya zama dandalin karuwai.

8. Hoto: Yan Najeriya sun dara ganin Obasanjo na shan Ice cream.

Yan Najeriya sun dara sosai ganin wasu hotuna dake nuna Obasanjo yana shan Ice Cream a Green Legacy Resort, a Abeokuta.

9. Shehu Sani ya bada sharudda akan yin sulhu da yan Boko Haram.

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsaki ya bayyana goyan bayan shi akan duk wani sulhu da shugaba Buhari ke niyyar yi da kungiyar Boko Haram.

Source: Legit.ng

Online view pixel