Manyan Labarai Guda 10

Manyan Labarai Guda 10

Legit.ng ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Alhamis 8, ga watan Oktoba. Ku duba domin samun su.

Manyan Labarai Guda 10
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (yana sama) da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki (yana kasa)

[article_adwert]

1. Saraki Ya Bayyana Manufar Zaman Su Da Buhari

Shugaban Majalisar Najeriya, Bukola Saraki ya bayyana cewa sun gana me da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin su hada hannu wajen cigaban Najeriya.

2. Cif Edwin Clark Ya Maganta Akan Jonathan Bayan Ya Bar PDP

Cif Edwin Clark, tsohon Kwamishinan Labarai na tarayya ya maganta akan Jonathan bayan daya fita daga PDP.

3. Tsofaffin Tsagerun Nija Delta Sun Baci Edwin Clark Saboda Ya Bar PDP

Kungiyar Niger Delta Liberation Force (NDLF) ta gaya ma Cif Edwin Clark yayi shiru bayan da ya bar PDP ya soki Jonathan.

4. Wike Ya Kori Ciyamomin Kananan Hukumomin Rivers

Gwamna Wike Na Jihar Rivers ya kori Ciyamomi 22 cikin 23 na kananan hukumomin Jihar Rivers.

5. Zaben Ministoci: Wadanda Aka Kai Sunayen Su Sun Fara Zuwa Majalisa

Domin tabbatar da bin tsarin tantance war, wadanda aka bada sunayen su sun fara zuwa majalisa suna kai takardun su.

6. Sanatoci Na San Amaechi - APC Din Rivers

APC ta Jihar Rivers ta bayyana jin dadin ya game da yadda sanatoci suka tsaya bayan Amaechi bayan da wasu suka soke shi a majalisa.

7. Tsohon Ciyaman Na PDP A Ondo Yaki Amsar Sabon Nadi

Ebenezer Alabi, tsohon Ciyaman din Jam'iyyar PDP ta Jihar Ondo yaki amsar sabon nadin da akayi mashi a jihar.

8. Oluremi Tinubu Ta Maganta A Majalisa

Oluremi Tinubu, matar Ahmed Bola Tinubu tayi maganarta ta farko a majalisar dattawa inda ta Kira Saraki, "Mai girma shugaban majalisa."

9. Yadda Wani Mai Gadi Ya Harbe Kanshi Da Bindiga

Ogundare Ekundayo wani mai gadi kusa da unguwar Ebute Metta harbe kanshi da bindiga bayan da yayi kokari ya tsorata barayi.

10. Enyeama Yayi Murabus Daga Buga Wasa Kasashen Waje

Dan wasa mai kare raga na Super Eagles, Vincent Enyeama yayi murabus daga buga wasannni a kasar waje bayan da suka samu rudani da koci Sunday Oliseh.

Source: Legit.ng

Authors:
Khadijah Thabit avatar

Khadijah Thabit (Copyeditor) Khadijah Thabit is an editor with over 3 years of experience editing and managing contents such as articles, blogs, newsletters and social leads. She has a BA in English and Literary Studies from the University of Ibadan, Nigeria. Khadijah joined Legit.ng in September 2020 as a copyeditor and proofreader for the Human Interest, Current Affairs, Business, Sports and PR desks. As a grammar police, she develops her skills by reading novels and dictionaries. Email: khadeeejathabit@gmail.com

Online view pixel