An bayyana sabon labari akan kungiyar Izala

An bayyana sabon labari akan kungiyar Izala

- Ana ruwaito akan shawari ga jaridar Rariya da sauran jaridu da yan jaridu da masu aiki irin nasu

- Ana cewa wanda, idan fasiki yazo muku da wani labari, kuyi bincike ku tabbatar kafin ku yada (watsa), kada kuyi abu bisa rashin sani ku dawo kuna da-na-sani

- An rahoto wanda jaridar Rariya basu yi binciki ba akan ingantaccen tarihin kungiyar Izala

A ranar Talata 12, ga watan Afirilu ne jaridar Rariya ta rubuta cewa: “Manufar kafa kungiyar Izala a Najeriya da sauran kasashe.”  Inda ana ci gaba da bayani, cewa, kuma sun nuna cewa daga dandalin Jibwis Najeriya aka turo musu.

Ya kamata Dan jaridar da yasan aikinsa ya tabbatar da gaskiyar Abu kafin ya watsa a cikin jama'a. Tabbas wannan rubutu da akayi da Sunan tarihin izala yana cike da Son Zuciya, Rashin bincike, Da shaida na zur.

Duk mai hankali Masanin tarihi yasan cewa idan aka samu kungiya, Ko Daula, Dole za'a samu wanda ya Assasa shi (Founder /pioneer),

Misali Shehu Usman Ibn Fodio shine ya kafa daular Usmamiyya.

Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab shi ya jagoranci jaddada sunnah a Saudiyya. Kuma da musulmai da arna sun tabbatar cewa ASH SHEIKH ISMAIL IDRIS BIN ZAKARIYYA ne ya kafa kungiyar izala, har mushrikai suke cewa yan izalah masu addinin da tsohon Soja ya assasa. Amma tsaban son Zuciya kun ki yarda cewa ASH SHEIKH ISMAIL IDRIS ne ya kafa kungiyar.

A cikin rubutun da kukayi kunce farkon alaramma na izala shine Sheikh Alhassan Saidu, wannan maganar ba haka yake ba. Ash Sheikh Alhassan Saidu Adam yana cikin alarammomi na farko a kungiyar, Amma akwai wanda ya rigaye shi.

Farkon Alaramma shine Alaramma Malam Musa Dan kaho. Na'am duk lokacin da kukayi rubutu akan tarihin izala, sai kuce Alhassan Saidu ne alaramma na farko, Duk da ba haka bane, amma son Zuciya sai ya hanaku fadin Sunan malami mai fassara na farko a kungiyar wato ASH SHEIKH ISMAIL IDRIS BIN ZAKARIYYA, shine malamin farko a tafiyar, Anyi lokacin da yake wuni wa'azi shi kadai, daga baya ya samu alarammomi masu taimakawa, Daga baya ya samu Malamai masu taya shi wa'azi,

Shine ya fara wa'azin, shine ya sakawa kungiyar suna jama'atu izalatil Bid'a sai Malaminsa Ash Sheikh Abubakar Gumi ya kara da Wa iqamatissunnah, shine ya fara jagorantar wa'azin kasa, shine hukuma ta daure shi fiye da sau talatin akan izala, shine aka je inda yake wa'azi aka bude wuta, aka harbi jama'a, Allah Ya tsare shi, shine lokacin da ake neman register ga kungiyar, Gwamnati ta saka wasu daga cikin malaman kasar nan suka neme shi suka masa interview akan hukunce hukuncen addini, sai wani yace hakika Sheikh Ismail Idris malami ne don haka ayi masa register ga kungiyar sa.

Shine yayi kaza da kaza, Allah ne kadai yasan gudumawarsa wajen assasa wannan kungiyar. Bayani ga yan tsalle tsalle, akan wannan rubutu da kuka turawa jaridar Rariya. A ciki kunce: Farkon shugaban izala Alhaji Musa Maigandu, idan kun manta mu tuna muku idan baku sani ba mu sanar daku.

Farkon Shugaban gudanarwa na farko a wannan tafiyar shine Alhaji Saleh Ahmadu Kaura Namoda. Kafin Alhaji Musa Maigandu. Amma tun farawar tafiyar Ash Sheikh Ismail Idris Bin Zakariyya ne yake jagoranta, tun ba'a sakawa kungiyar suna ba,

Kunce Kungiyar musulunci ne da musulmi suka kafa. Tabbas Kungiyar Musulunci Ne Na Musulmai, Amma Sheikh Ismail Idris Ne Ya Kafa. Kunce tana da hedikwatar a Jos. Sannan tana da ofishin tuntuba a Abuja, inda nanne ofishin shugaban ta na kasa yake a halin yanzu.

Ya kamata kusan cewa da masu hankali kuke magana. Hedikwatar yana Jos amma ofishin shugaban yana abuja, kamar dai kace fct abuja ne babban birnin tarayya, amma ofishin shugaban kasa yana Katsina.

Abin dariya, inda shugaban kungiyar ne na gaske, ba shugaban tsalle tsalle ba, to tabbas ofishin sa Zai kasance a hedikwatar na Kungiyar koda Zai rika zuwa lokaci bayan lokaci To sunce headquarter na Jos, Amma ofishin Shugaba na Abuja. Wannan ba shine shugaban kungiyar na gaskiya ba. Shugaba yana zama ne a headquarter, Kuma ko baya garin da zama, dole a samu ofishin sa a headquarter kuma ya rika zuwa yana aiki lokaci bayan lokaci.

Kunce Abubuwanda kungiyar ta maida hankali a kansu: Tana gabatar da wa'azin kasa a ko wane mako biyu ko uku ko hudu. Wannan ya tabbatar mana da cewa Ash Sheikh Muhammad Sani Alhaji Yahya Jingir da mataimakin sa Ash Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun. Sune halatattun shugabannin izala domin bayan sati uku - uku suke jagoranta jama'a zuwa wa'azin kasa..

Amma yan tsalle tsalle sunyi kusan shekaru biyu basuyi wa'azi ba, sai kwanaki da sukayi a Abuja. To wadanda suka shekara biyu basuyi waazin kasa ba Ashe ba sune yan izala ba. Kunce tarihin izala bazai manta da gudumawar Sheikh ismail Idris ba. To masu zagin Sheikh ismail Idris, masu bid'antar dashi, Irin su kabiru Gombe da yace yan Ismailiyya yan Bid'a, har yake kwatanta muryar Sheikh Ismail Idris a garin Ibbi etc. Irin jalo jalingo da ya rubuta littafin zuwa ga yan ismailiyya yana zagi da bid'antar da Sheikh Ismail Idris.

ASHE SU BA YAN IZALA BANE

Don haka shugaban majalisar Malamai na izalah na gaskiya shine ASH SHEIKH MUHAMMAD SANI ALHAJI YAHYA JINGIR, Kuma shine jagoran kungiyar domin baya zagin Sheikh Ismail Idris, Amma, Jalo Jalingo Shugaba ne na yan tsalle tsalle, domin yana zagin Sheikh Ismail Idris. Kabiru Gombe ba shine Secretary General na Kungiyar na gaskiya ba, domin yana zagin Sheikh Ismail Idris. Shin suma yan izala ne, Don munga suna zagin Sheikh ismail Idris?

Izalar asali mai hedkwata a Birnin Jos wanda ASH SHEIKH Sani Yahaya Jingir yake jagoran ta, ta Gina makarantu fiye da dubu daya 1,000, Kuma akwai dalibai miliyoyi a Nigeria da wajen ta. Akwai ASAS PRIMARY, MALJAU SSUNNAH, DIPLOMA, NCE, da sauran su. Amma yan tsalle tsalle masu karyar izala su fada mana makarantu nawa suke dasu?

Kunce Sheikh Alhassan Saidu shine farkon alaramma a I zala.Haka ne? A'a. Farkon Alaramma shine, Alaramma Malam Musa Dan kaho.

To waye ne farkon mai fassara a izala? Son Zuciya ya hanaku fadi. Ashe akwai wanda ya assasa tafiyar, Kuma shine mai fassara na farko. Ku tambayi Sheikh Alhassan Saidu ya fada muku wanda yake jawa Baqi (Mai Fassara na Farko). Anyi Taron Kafa Kungiyar Izala A Headquarter Na Kungiyar A Jos, A Filin Stadium,

ranar Lahadi 12-03-1978. Kuma Ash Sheikh Isma'il Idris ne babban jagora lokacin taron.

KU KARANTA KUMA: Dogon tarihin akan manufar kungiyar Izala a Najeriya

Wanene ya kafa Izalah shidai Sheikh Ismaila Idris bn zakariyya wani Malami ne Kuma Soja ne da Allah yayi wa Al'ummar Musulmi. Baiwa dashi. Domin Malami ne da Allah ya cire masa tsoro wajen fito da Al'amari yadda yake, domin bayyanar sa ce ta fito da Munanan Akidu na Shirka da Bidi'oi da ake aikatawa da Sunan Musulunci a wannan kasa Mallami ne da Allah ya masa baiwa na Ilmunmuka Daban-daban kama daga kan Akida, Fiqhu, Hadisi, Lugga, Tafsir Mallamine da ya sha ya Koshi.

Mallam yayi Mukabala da Mushrikai da 'Yan Bid'a Daban-daban. Kuma Allah yana bashi Nasara ya kayar da su da Hujjoji daga Qurani da Hadisi. A wancan lokaci Akwai Mallamai A wannan kasa Amma basu iya tashi sun fito da Munanan Akidun nan a fili ba, Sai da Allah ya bayyanar da Sheikh Ismaila Idris Ya fara fito da Munanan Akidu. Musamman na Darikun Sufaye a fili. Inda Yaci gaba da karantar wa karkashin Al Qur' ani da Hadisi, kamar yadda Sheikh Abubakar Mahmud Gummi ya fada a littafinsa 'Manufata Shafi na 184'. Allah ya taimaki Sheikh Ismaila Idris da karantarwar Sunnah,

Allah ya bashi ikon kafa kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Ikamatis Sunnah' a ranar 12 ga watan Maris a 1978 a garin Jos, kamar yadda daya daga cikin Almajiransa Sheikh Alhassan Said Jos ya fada, a duba (Mujallar Alburhan Adadi na 39 Shafi na 12).

Sheikh Abubakar Gummi da kansa yake cewa, 'Aikin da Sheikh Ismaila Idris yayi yafi nawa karfi domin ni kadan-kadan nakeyi,...Har na zama Uba Gareku, kaset na Gaisuwar Sallah ga Sheikh Gummi 1984. Sheikh Ismaila Idris An Rufe Shi a Gidan kurkuru Yafi a kirga

Sanadiyyar tsayuwa don Gusar da Shirka da Bid'a da tabbatar da Sunnah a wannan kasa. Mallam Uba ne ga kowane Mallami ko Dalibi Dake Da'awar Sunnah a wannan kasa. Wannan Yasa tunda Mallam ya koma ga Allah Kullum Sai Anyi Masa Adduar Alkhairi. Sheikh Ismaila Idris ya rasu ranar 22 ga Janairu a 2000.

Muna rokon Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya sanya ayyukansa na Alkhairi a Mizanin Lada, Ya Hadamu A Gidan Aljannatul Firdausi,...

Allah ja jikan Sheikh Albani Zaria yace Ash Sheikh Ismail Idris Bin Zakariyya ne ya kafa kungiyar Izala, kuma duk Ahlusunnah na wannan nahiyar ya amfana da haske daga Ash Sheikh Ismail Idris Bin Zakariyya, Sheikh Albani Zaria yayi wannan maganar a Wa'azin Izala na kasa a Zaria da farin Sako da wasu wuraren dabam.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel