Kungiyar Izalatil Bid'ah sun ziyarci Khalifah Tijjaniyya

Kungiyar Izalatil Bid'ah sun ziyarci Khalifah Tijjaniyya

- Yan kungiyar Izalatil Bid'ah wa Iqamatus Sunnah a jihar Kano sun ziyarci wani Khalifah Tijjaniyya na nahiyar Afirika gaba daya, Sheikh Isyaku Rabiu

- Sheikh Isyaku Rabiu yake farin cikin saboda ziyara

- Wani manyan mai wasi mai suna Dakta Abdallah Saleh daga kasar Pakistan, shine ya kai tawagar kungiyar

Rahotanni na nuna cewa daga jaridar Rariya wanda, kungiyar Izala ta jihar Kano, ta ziyarci wani Khalifah Tijjaniyya na nahiyar Afirika, mai suna Sheikh Isyaku Rabiu

A daren Laraba 23, ga watan Maris da misalin karfe 9:30 na dare, shugaban kungiyar Izala ta jihar Kano, Dakta Abdallah Saleh Pakistan ya jagoranci tawagar kungiyar domin kai wa Khalifan Tijjaniyya na Afrika ziyara wato Khalifah Isyaku Rabiu.

Kungiyar Izalatil Bid'ah sun ziyarci Khalifah Tijjaniyya
A lokacin ziyarar kungiyar Izala a gidan Sheikh Isyaku Rabiu

Acikin tawagar ta kungiyar Izala akwai sakataren kungiya, shugaban agaji, mataimakin shugaba, 'yan majalisar zartarwa, da wakilan kananan hukumomi na jihar Kano. Sannan daga cikin wadanda suka karbi wannan tawaga sun hada da Babban limamin masallacin Juma'a dake Kofar Mata, Sheikh Nasir Adam, Shehi Shehu Maihula da sauransu.

Tun farko, Sheikh Nasir Adam shine ya yi jawabin maraba ga baki, kana daga baya ya mika abin magana ga sakataren kungiyar Izala na Kano, Imam Ali Aliyu Abubakar wanda shine ya gabatar da wadanda suka je ziyarar, kuma ya gabatar da Shugaban Izalar Kano Dakta Pakistan domin ya yi nasa jawabin.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Kabiru Gombe ya maganta akan Izalatil Bid’ah

Acikin jawabin nasa, Dr. Pakistan ya bayyana makasudin wannan ziyara shine abubuwa guda uku:

1. Duba lafiyar halifa Isyaka Rabi'u bisa jinya da ya yi.

2. Waliktar shugaban Kungiyar Izala na kasa domin a yi ban gajiya ga Halifa Isyaka Rabi'u bisa wakilcin da ya tura taron da kungiyar Izala ta gabatar a garin Abuja.

3. Tattaunawa akan wasu muhimman abubuwa da za su ciyar da addini gaba.

Kungiyar Izalatil Bid'ah sun ziyarci Khalifah Tijjaniyya
Acikin gidan Sheikh Isyaku Rabiu
Kungiyar Izalatil Bid'ah sun ziyarci Khalifah Tijjaniyya
Manyan Musulmai guda biyu

Kuma Daktar Pakistan ya yi bayani daki-daki akan kowanne daga cikin abubuwan guda uku. Kuma daga baya ya karkare jawabin nasa da wadansu maganganu na hikima da sanin ya kamata.

A nashi jawabin, Khalifah Isyaku Rabiu, ya bayyana matukar jin dadinsa ga wannan ziyarar da aka kawo masa, kuma ya yi alkawarin rike wannan zumunci dake tsakani, da kuma tattaunawa da kungiyar Izala akan duk wani abu mai muhimmanci da zai iya tasowa.

A karshen jawabin nasa ne, Khalifah ya gabatar da kyauta irin ta mutuntawa ga tawagar kungiyar kuma ya yi kalamai na yabo da jinjina gare su. Sannan yayi addu'a ga wannan tawaga mai albarka.

Idan ba a manta ba, wannan ita ce ziyara ta hudu da kungiyar Izala ta kai wa Khalifan Darikar Tijjaniyya na Afrika da Khalifan Kadiriyya na Afrika kuma tana takawa ne ta je har gida ta same su, wannan ya nuna cewar kungiyar tana cike da son hadin kai tsakanin al'ummar Musulmi.

Source: Legit.ng

Online view pixel