Yan Boko Haram sun farma garin Bita

Yan Boko Haram sun farma garin Bita

- Sun farma sojojin Najeriya bazata

- An kwana yana yaki

- Sojin sama ta kai agaji

Yan Boko Haram sun farma garin Bita da yaki inda aka kwana ana musayar wuta dasu da sojojin Najeriya. Yan kungiyar sunyi yunkurin amshe Bita domin yana da muhimmanci kuma kusa yake da garin Gwoza, wanda ya taba zama Hedikwatar kungiyar.

KU KARANTA: Sojojin Kasar Kamaru Sun Shigo Najeriya, Sun Kashe Mutane 150

Wannan lamari ya faru ne a ranar 7 ga watan Maris na 2016. Sojin Najerya dake garin Bita ne suka rike yan ta'addan da yaki. Yan ta'addan sun kusa mamaye Bita amma sai sojojin sama na Najeriya suka kawo ma na kasa agaji inda aka murkushe yan ta'addan gaba dayan su.

Sojojin Najeriya sun sha alwashin cewa zasu kare Gwoza da sansanin yan gudun hijira dake a garin kuma baza su bari yan kungiyar Boko Haram su sake amshe garin ba. Jaridar Dailytrust ta ruwaito labarin.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun samu nasara akan Boko Haram

Idan za'a iya tunawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta murkushe Yan Boko Haram. Ya bayyana haka ne a watan Disambar data wuce ta 2015 bayan daya ba sojin Najeriya wa'adi su kawo karshen yakin.

Source: Legit

Mailfire view pixel