Manyan Labarai Guda 9

Manyan Labarai Guda 9

Kada ku rasa manyan labaran da sukayi fice a kowace rana. Legit.ng na tattara maku su a kullum. Ku duba kuga manyan labaran da sukayi fice a ranar Laraba 19 ga watan Agusta.

[article_adwert]

1. Anyi watsi da rokon dan takara APC na Jihar Rivers.

Kotun sauraraon kara ta zaben Jihar Rivers wadda dake zama a Abuja wadda Mai Shari'a Mu'azu pindiga yake jagoranta tayi watsi da rokon da dan takarar Jihar Rivers yayi.

2. Shugaba Buhari za yayi babban Bako.

Banki Moon, Sakataren majalisar Dinkin Duniya zaya ziyarci Buhari a ranar 23 ga watan Agusta.

3. Wani dan shekara 23 na iya zama Sarki Ife.

Bayan mutuwar Sarki Sijuwade Okunade, ana tsammanin wani dan shekara 23 ya maye gurbin sa.

4. Shugaba Buhari ya kori Almustapha Chike-Obi.

A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori shugaban Kamfanin kula da kaddarori na kasa (AMCON) daga aiki.

5. Osinbanjo ya bayyana yawan Yan Najeriya dake cikin talauci.

A jiya ne Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbanjo ya bayyana yawan Yan Najeriya da talauci yake addaba.

6. Buhari zaya rage kudin mai.

A wata fira da akayi da Mai taimaka ma shugaban kasa akan hudda da Jama'a, Shehu Garba, ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya a karkashin Buhari zata hada kai da masu shigowa da Mai domin rage kudin Man.

7. Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram.

Sojojin Najeriya na agajin gaggawa na 26 dake Gwoza sun kashe mayakan Boko Haram da yawa a lokacin da Sojojin sama sukayi masu ruwan bama-bamai, cewar Sani Usman, Jami'i mai kula da labarai.

8. Tsohon shugaban Majalisar Dattawa zaya canza sheka zuwa APC.

Masu jigajigan Jam'iyyar PDP dake Jihar Cross River zasu canza sheka su koma APC.

9. Jonathan da iyalinsa na Kenya suna shakatawa.

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan tare da iyalinsa na Kasar Kenya suna shakatawa. Wata Jaridar Kasar ta Kenya ta saki wasu hotuna na tsohon shugaban Kasan.

Source: Legit.ng

Online view pixel